TASIRIN MAƘOTA NA GARI


Amon ‘labbaikallahumma labbayka’ ne yake tashi a karo na uku daga wayar Alh. Bello, cikin hanzari ya ɗaga “Mal. Auwal afuwan!” Ashe Mal. Auwal ne maƙocinsa zusu je ɗaurin auren ladanin unguwarsu a yau Asabar wanda za a yi ƙarfe 11ns. Fitowar Alh. Bello kenan, ya tadda Mal. Auwal zaune cikin motarsa yana jiransa. Fara tafiyarsu ke da wuya Alh. Bello yace “Akwai buƙatar na sayi wani abu a danja domin ban ƙarya ba. Amarya tana bacci da ƙyar ta samu tace min a dawo lafiya cikin magagi”.

Tausayin Alh. Bello ne ya kama Mal. Auwal domin shi kuwa tun da suka tashi sallar Asuba matarsa Zainabu ta saka alarm, ta tashi da wuri, ta tashe shi yayi wanka inda ta riga ta kai masa ruwan wanka bayi. Fitowarsa ke da wuya, ya riski buɗa baki yana jiransa. Cikin nishaɗi suka karya suna hira daga bisani ya fara kiran Alh. Bello. Tabbas akwai tawaya cikin kulawar da Alh. Bello yake samu daga uwar ɗakinsa Bikisu. Haka Mal. Auwal yayi ta saƙe-saƙe, tinanin yanda zai taimakawa abokinsa domin inganta rayuwar aurensa. Bayan sun dawo ya gayawa matarsa kasancewar suna kusa akan akwai buƙatar cikin hikima ta nusashshe da matar Alh. Bello akan zamantakewar aure.

Washegari da yamma, wato ranar bikin ladan, Bilkisu matar Alh. Bello tare da Zainabu matar Mal. Auwal da Hajiya Hanne, gwaggon ango ladan zaune suke a ɗaki guda suna ta hira abinsu. Can sai Hajiya Hanne tace zata je dubiya bayan layi gidan sirikarta Hajiya Rabi’atu wacce zazzaɓi ya sako ta a gaba ga kuma tsufa. Caraf Bilkisu tace za ta je ita ma ta dubata.

Zainabu kuwa tace sai sun dawo domin ba ta tambayi mai gidanta ba kuma tin da ba gaggawa ake ba, za ta bari idan ya dawo sai ta tambayeshi sannan ta je. Bilkisu sai cewa tayi; “Nima ban tambaye mijina ba, amma ai aikin lada ne, gaida mara lafiya fa akace za a je.” Zainabu kuwa ce mata tayi ai miji yana da haƙƙin sanin duk inda matarshi zata sa kafarta ko da kuwa kofar gidane, ballantana shiga maƙota. Nan kuwa Hajiya Hanne tace; “Hakane, domin kuwa idan wani abu ya faru da mace, ba fata ba, a inda mijinta bai san da zuwanta ba, hakan zai rushe aminci dake tsakaninsu, kuma amana ginshiƙi ce a aure.” Daga nan Zainabu ta kara faɗaɗa jawabi akan mahimmanci neman izini a wajen mai gida kafin fita da sauran mu’amala ta yau da gobe.

Bayan Hajiya Hanne ta tafi dubiyarta suka cigaba da taɗi akan abin da ya shafi kulawa da miji inda ta samu damar wayarwa da Bilkisu kai sosai. Daga nan ta nuna mata cewa matuƙar bata maida hankali ta koyi dabarun kulawa da mijinta ba, to akwai barazanar ya samu wata majalisa da zata cike masa wannan gurbin, kuma hakan ma zai fara saka shi gaggauta tinanin samo mata abokiyar zama wacce yake ganin zata fita. Bilkisu godiya ta yiwa Zainabu da ƙara godewa Allah da ya haɗa su maƙwabtaka tare. 

Comments

Popular posts from this blog

'SANIN MANUFAR RAYUWA SHI NE RIBAR ZUWA DUNIYA' NA KHADEEJAH MUHAMMAD DAYYEEB

THE END OF POVERTY BY JEFFREY SACHS

TOWARDS SUSTAINABLE WASTE MANAGEMENT APPROACH IN KANO METROPOLIS: LESSONS FROM MUSLIM CITIES