Posts

Showing posts from November, 2022

TASIRIN MAƘOTA NA GARI

Amon ‘labbaikallahumma labbayka’ ne yake tashi a karo na uku daga wayar Alh. Bello, cikin hanzari ya ɗ aga “Mal. Auwal afuwan!” Ashe Mal. Auwal ne ma ƙ ocinsa zusu je ɗ aurin auren ladanin unguwarsu a yau Asabar wanda za a yi ƙ arfe 11ns. Fitowar Alh. Bello kenan, ya tadda Mal. Auwal zaune cikin motarsa yana jiransa. Fara tafiyarsu ke da wuya Alh. Bello yace “Akwai bu ƙ atar na sayi wani abu a danja domin ban ƙ arya ba. Amarya tana bacci da ƙ yar ta samu tace min a dawo lafiya cikin magagi”. Tausayin Alh. Bello ne ya kama Mal. Auwal domin shi kuwa tun da suka tashi sallar Asuba matarsa Zainabu ta saka alarm , ta tashi da wuri, ta tashe shi yayi wanka inda ta riga ta kai masa ruwan wanka bayi. Fitowarsa ke da wuya, ya riski bu ɗ a baki yana jiransa. Cikin nisha ɗ i suka karya suna hira daga bisani ya fara kiran Alh. Bello. Tabbas akwai tawaya cikin kulawar da Alh. Bello yake samu daga uwar ɗ akinsa Bikisu. Haka Mal. Auwal yayi ta sa ƙ e-sa ƙ e, tinanin yanda zai taimakawa abokinsa d...

GUDUNMOWAR SOSHIYAL MIDIYA WURIN CIGABAN ADABIN BAHAUSHE

Image
  Soshiyal midiya wacce ake fassarawa da ‘kafafan sada zumunta na zamani’ ta taimaka wajen tallanta adabin Bahaushe ta hanyoyi da dama, kama daga rubututtuka wa ɗanda suka haɗa da sa ƙ onni, gajerun labarai, wa ƙ o ƙ i har izuwa wasanni kwaikwayo. Ta kuma ƙara fito da al'adun Hausawa fili, tare da tagomashin samar da rana guda kacokan domin bajakolin yaren Hausa a sanadin soshiyal midiya.   Zuwan soshiyal midiya ya ha ɓ aka yawan rubututtuka da Hausawa da sauran ma'abota aiki da yaren Hausa suke yi. Domin kuwa a kullum, mutane suna amfani da wa ɗ annan kafafan sadarwa wajen aikawa da kar ɓ ar sa ƙ onni cikin harshen Hausa, musamman a kafar sadarwa ta WhatsApp da Facebook Messenger. Hakanan, an samu, kungiyoyi da zaurukan wanda suke da ala ƙ a da adabi da suke amfani da soshiyal midiya wajen gudanar da kuma ha ɓ aka shirye-shiryensu. Misali, akwai gasar rubutacciyar wa ƙ a da ake a dandalin sada zumunta na Facebook da akewa take da 'Asabe' wanda yake zaburar da m...