GUDUNMOWAR SOSHIYAL MIDIYA WURIN CIGABAN ADABIN BAHAUSHE
Soshiyal midiya wacce
ake fassarawa da ‘kafafan sada zumunta na zamani’ ta taimaka wajen tallanta adabin
Bahaushe ta hanyoyi da dama, kama daga rubututtuka waɗanda suka haɗa da saƙonni,
gajerun labarai, waƙoƙi har izuwa wasanni kwaikwayo. Ta kuma ƙara fito da
al'adun Hausawa fili, tare da tagomashin samar da rana guda kacokan domin bajakolin
yaren Hausa a sanadin soshiyal midiya.
Zuwan soshiyal midiya
ya haɓaka
yawan rubututtuka da Hausawa da sauran ma'abota aiki da yaren Hausa suke yi.
Domin kuwa a kullum, mutane suna amfani da waɗannan
kafafan sadarwa wajen aikawa da karɓar
saƙonni
cikin harshen Hausa, musamman a kafar sadarwa ta WhatsApp da Facebook
Messenger. Hakanan, an samu, kungiyoyi da zaurukan wanda suke da alaƙa
da adabi da suke amfani da soshiyal midiya wajen gudanar da kuma haɓaka
shirye-shiryensu. Misali, akwai gasar rubutacciyar waƙa
da ake a dandalin sada zumunta na Facebook
da akewa take da 'Asabe' wanda yake zaburar da mutane wajen rubuta waƙoƙi
a kowacce Asabar, da sauran makamantan shirye-shirye irin wadanan.
Bugu da ƙari,
a yanzu, dandalin sada zumunta na Facebook,
wanda shine babbar kafar sada zumunta ta duniya yana da kimanin mutane biliyan
uku (Data Reportal 2022), kuma akan wannan kafa, akwai yaren Hausa cikin jerin
yarika da mutum zai iya amfani dasu wajen sarrafa wannan manhajja ta Facebook, kamar yadda zai iya amfani da
Turanci, Larabci, Faransanci da sauran manyan yare da ake amfani dasu a duniya.
Wannan ya ƙara
ɗaukaka
adabin Hausa a idon duniya baki ɗaya.
Hatta waɗanda basu san menene yaren Hausa ba, sanadiyyar
soshiyal midiya a yau, samun wayewar kai akansa. Hakanan akan ragowar waɗansu
daga cikin saura kafofin za ka samu yaren Hausa ya samu gindin zama.
Wani abin alfahari da
soshiyal midiya ta haifarwa adabin Hausa a yau shine rana ta musamman da aka ƙirƙira
a dalilin kafafan sada zumunta domin tinawa da Harshen Hausa a duniya, wato 26
ga watan kowanne Agusta. Hakan ya janyo hankalin mutane a duniya da dama akan adabin
Hausa ta yadda Hausawa da suaran masu amfani da harshen Hausa suke bajakolin maganganu
cikin hikima, da amfani da karin magana da waƙe da habaici da zambo
da sauran fannoni na adabin Hausa domin nuna bajinta da alfahari da harshen
Hausa a wannan ranar. Tabbas, wannan abin akwai banƙaye
acikinsa, kuma ba a nan kawai ya tsaya ba, ƙasashe irinsu su Najeriya, Ghana,
Chadi, Nijar suna haɗa taruka na musamman domin gabatar da jawabai da maƙaloli
akan muhimmancin adabin Hausa. Wannan duka yana faruwa sanadiyyar wata gaɓara
da ta faro ne daga soshiyal midiya.
Sannan soshiyal
midiya tana taka muhimmiyar rawa wajen koyo da koyarwa na adabin Malam
Bahaushe. Akwai shafuka yanzu waɗanda aka ƙirƙiro
akan kafafan sada zumunta na zamani domin koyar da wasu fannoni na adabin Hausa.
Sannan akwai masana akan adabin Hausa suma da suke amfani da shafukansu wajen
daɗa
ilimantar da mutane akan abubuwa daban-daban domin ƙara
wayarwa da al’ummar Hausawa kai. Hakanan kuma, akwai zauruka da ake ƙirƙira
musamman a kafar sada zumunta ta WhatsApp
domin koyar da adabi da kuma gudanar da wasu shirye-shiryen domin haɓaka
adabi. Ya isa misali zauren WhatsApp
na kungiyar marubuta ta ƙasa reshen jihar Kano (ANA KANO), da sauran
zauruka da dama waɗanda ake buɗewa
domin koyar da rubutacciyar waƙa, da waɗanda ɗaliban
adabin Hausa suke buɗewa domin taimakawa nazarinsu, da
sauransu.
Waɗannan,
dama sauran abubuwa waɗanda suka haɗa
shirye-shirye na musamman akan soshiyal midiya lokaci bayan lokaci waɗanda
suke ƙara
karkato da hankalin mutane izuwa kan adabin Hausa, tare da taimakawa matuƙa
gaya wajen ƙara
tallata ƙungiyoyi
da mutane da suke da alaƙa da adabi, hatta ƙungiyar marubuta ta ƙasa
(ANA) ta samu tagomashin tallata ayyukanta da kuma gudanar da shirye-shiryenta
ta hanyoyi mabanbanta akan soshiyal midiya tare da adana bayanai domin waɗansu
su amfana ko kuma su kalla ko saurara alhali basa inda ake gabatar da
shirye-shiryen. Wannan duka sun samu ne sanadiyyar soshiyal midiya.
Comments
Post a Comment