'SANIN MANUFAR RAYUWA SHI NE RIBAR ZUWA DUNIYA' NA KHADEEJAH MUHAMMAD DAYYEEB
Littafi ne mai shafuka 66
wanda Markazut-Tarbawi Al-Islamee, Kano, Nigeria suka wallafa shi wanda yake
cike da wa'azi mai shiga zuciya da kuma cikakkiyar tinatarwa cikin taƙaitattun
kalmomi a kan manofofin rayuwarmu ta duniya, da kuma yadda za mu ribace ta.
Malama Khadeejah ta buɗe
littafin ne da bayani a kan tsarin matakan rayuwar ɗan
adam inda ta kasa ta zuwa matakai guda huɗu
1. Rayuwar
ɗan
adam a cikin mahaifiya
2. Rayuwar
ɗan
adam a Duniya
3. Rayuwar
ɗan
adam a barzahu, da kuma
4. Rayuwar
ɗan
adam a Lahira
Rayuwar
Cikin Mahafiya
Malama Khadeejah ta yi
bayani musamman abin da ya shafi ma'anar wannan rayuwar da kuma abubuwan da
suke faruwa kamar yadda Manzon Allah SAW ya yi bayani tun ɗan
adam yana maniyyi, da kwanakin da yake ɗauka
ya zama gudan jini, gudan tsoka, har zuwa a busa masa rai, da ma lokacin da za
a haife shi tare da darussan da suke ciki; musamman irin taƙaitaccen
lokacin da ɗan adam yake a wannan mataki na rayuwa da
bai wuce ƴan watanni ba.
Rayuwar
Duniya
Matakin na biyu kuma wato
rayuwar duniya, Malama Khadeejah ta yi jawabi tare da jan hankali a kan irin
yadda Allah SWT ya umarce mu da mu gudanar da ita, cikin neman kusanci zuwa
gareshi, ta hanyar biyayya ga dokokinsa da ya shimfiɗa
mana ta hanyar manzonsa, Annabi Muhammad SAW. Ta kuma maida hankali matuƙa
wajen ƙoƙarin
fahimtar da mai karatu cewa rayuwarsa ta duniya, wata jarrabawa ce da Allah
yake masa domin tantace gaskiyar imaninsa, ta yadda ɗan
adam zai maida dukkan ayyukansa, a matsayin hanyoyin bauta ga Ubangiji. Da kuma
nisantar saɓa masa tun daga kan nema, mu'amala, da kuma
kula da ibada. Ta kuma ja hankali a kan lalle kada mu shagala da abubuwan da za
su ɗauke
hankalinmu wajen bautawa Allah yayin gudanar da taƙaitacciyar
rayuwar duniya, wacce ba komai ba ce idan mutum ya haɗa
ta da ta Lahira.
Rayuwar
Barzahu
Rayuwar barzahu ita ma ta
yi cikakken bayani a kan ta tare da kawo hadisai da ayoyi kasancewar ta madagata
(rayuwar kabari) kafin isa zuwa Lahira. A wannan rayuwar mutum yake haɗuwa
da mala'iku da za su yi masa tambayoyi wanda amsa za ta fito gwargwadon yadda
bawa ya mu'amalanci addininsa a duniya. Ga wanda ya bi Allah, ya kuma nisanci
saɓa
masa, zai samu nasarar tsallakewa tare da samu yalwa a kabarinsa da kuma fara
samun tagomashi na rahama daga Allah SWT sakamakon ayyukan alheri da ya aikata.
Kafiri, da munafiki, da mujirimi kuwa, za su gaza amsawa, take kuma za su fara
fuskantar matsin kabari da kuma azaba har a tashi alƙiyama.
Daga cikin nau'in
munafurci da Malama Khadeejah ta zayyana mana akwai:
1. Faɗin
imani a baki tare da saɓa wa hakan a zuciya
2. Ƙaryata
Annabi SAW ko kuma wani abu da ya zo da shi; ta yadda mutum zai ji cewa waɗansu
tabbatattun hukuncin Musulunci ba adalci ba ne ko kuma jin saɓa
wa dokokin Allah ba wani abu ba ne
3. Yin
izgilanci ga sha'anin imani ko masu imani
4. Toshe
hanyar cigaban Musulunci
5. Jin
daɗi
yayin da wani abu mara daɗi ya samu muminai
Waɗannan
na daga cikin ɗabi'un munafiki da ya kamata mutum ya yiwa
kansa katangar ƙarfe daga afka musu domin
gujewa fushin Allah SWT.
Shi kuma fajiri shi ne mai
yawan aikata manyan laifuka a bayyane kuma cikin izgilanci. Kuma kamar yadda
muka gani a sama duka suna faɗawa cikin waɗanda
ba za su ci nasarar amsa tambayoyin kabari ba, duk da cewa, azaba tana komawa
gwargwadon yadda bawa ya saɓa wa Allah SWT matuƙar
bai yi kafirci ba.
Rayuwar
Lahira
Sai kuma rayuwar Lahira,
inda Malama Khadeejah ta maida hankali kacokan a kan Aljanna da kuma ni'imomin
da suke cikinta, musamman abin da ya shafi dawwama da kuma abubuwan jindaɗin
da suka sha ban-ban da abin da muka sani anan duniya. Malama Khadeejah ta yi
jawabi cewa rayuwar Aljanna ita ce rayuwar Lahira domin kuwa wutar Jahannama,
ba rayuwa ake a cikinta ba kuma ba mutuwa ake ba, kamar yadda Allah ya yi
jawabi cewa – “Ba a mutuwa a cikinta kuma ba a rayuwa.” Tabbas duk mai karatu
idan ya fahimci irin tanadin ni'imomin da Allah SWT ya yiwa bayinsa na gari a
Aljanna, babu makawa, ya sake ɗaura ɗaramar
kyautata tsakaninsa da mahaliccinsa.
Lokacin da Malama
Khadeejah ta dawo kan bayanin akan wutar Jahannama da irin narkon dake tare da
ita, dole zuciyar mai karatu ta raurawa tare da sake nisanta aikin da zai jefa
bawa cikinta. A cikin hikimar Allah SWT kuma ya kasance Lahira gida biyu
gareta, ko dai Aljanna, ko wuta, don haka duk bawan da ya shiga wuta, Malama
Khadeejah ta nusasshemu da cewa shi ya zaɓa,
domin an katse masa hanzari ta hanyoyi da dama musamman ta wuraren guda biyu da
ta yi mana jawabi kamar haka:
1. Aiko
manzo da saƙon Allah, da kuma
2. Gatan
iyaye: wanda Allah ya yiwa bayinsa cikin hikimarsa.
Kuma, Allah ya tsara cewa
ba zai tuhumi bawa ba face ya kai shekaru balaga, wanda kafin nan, gatan
tarbiya da iyaye za su ba shi ya ishe shi fahimta waye Allah kuma ta ya ya zai
bauta masa.
Daga ƙarshe
Malama Khadeejah ta yi tanbihi ta hanyar dubayya ga abubuwan da suke kamanceceniya
tsakanin rayuwar da ɗan adam yake yi a cikin
mahaifiya da kuma rayuwar barzahu, hakanan tsakanin rayuwar Duniya da ta
Lahira.
Tabbasa mai karatu ba zai
taɓa
wadatuwa da irin wannan gajerin lattafi ba mai cike da tasiri mai girma wajen ƙoƙarin
juya akalan al'umma zuwa abin da zai fisshe su Duniya da kuma Lahira. Haka nan
littafin ya rubutu cikin bin ƙa'idar rubutun Hausa wanda
hakan zai ba wa mai karatu damar karanta shi cikin sauƙi,
Allah Ya saka wa Malama Khadeejah da mafificin alherinsa, amin!
Comments
Post a Comment