Posts

Showing posts from September, 2025

'SANIN MANUFAR RAYUWA SHI NE RIBAR ZUWA DUNIYA' NA KHADEEJAH MUHAMMAD DAYYEEB

Image
  Littafi ne mai shafuka 66 wanda Markazut-Tarbawi Al-Islamee, Kano, Nigeria suka wallafa shi wanda yake cike da wa'azi mai shiga zuciya da kuma cikakkiyar tinatarwa cikin ta ƙ aitattun kalmomi a kan manofofin rayuwarmu ta duniya, da kuma yadda za mu ribace ta. Malama Khadeejah ta bu ɗ e littafin ne da bayani a kan tsarin matakan rayuwar ɗ an adam inda ta kasa ta zuwa matakai guda hu ɗ u 1.       Rayuwar ɗ an adam a cikin mahaifiya 2.      Rayuwar ɗ an adam a Duniya 3.      Rayuwar ɗ an adam a barzahu, da kuma 4.      Rayuwar ɗ an adam a Lahira   Rayuwar Cikin Mahafiya Malama Khadeejah ta yi bayani musamman abin da ya shafi ma'anar wannan rayuwar da kuma abubuwan da suke faruwa kamar yadda Manzon Allah SAW ya yi bayani tun ɗ an adam yana maniyyi, da kwanakin da yake ɗ auka ya zama gudan jini, gudan tsoka, har zuwa a busa masa rai, da ma lokacin da za a haife shi tare da darussa...